Home DUNIYA Najeriya za ta ci gaba da kwase ‘yan ƙasarta da ke Sudan...

Najeriya za ta ci gaba da kwase ‘yan ƙasarta da ke Sudan a yau Asabar

Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya da ta Jin-ƙai da agajin gaggawa sun ce a yau Asabar motoci 29 za su isa Sudan domin kwaso sauran ɗalibai da sauran ‘yan Najeriya da suka rage a ƙasar.

Cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar, ma’aikatun sun yi ƙarin haske kan halin da ake ciki game da ɗaliban Najeriya da rikicin Sudan ya rutsa da su.

Sanarwar ta shawarci waɗanda za a kwaso su tsaya a inda aka umarce su da kayan da za su iya riƙewa a hannu kawai, kada su yi amfani da irin abubuwan da suke yawo a kafafen sada zumunta.

Sanarwar ta ce wakilan ofishin jakadancin Najeriya za su kasance a Khartoum domin tabbatar da an kwashe ɗaliban da sauran ‘yan Najeriyar da ke birnin.

An kuma shawarce su da su tanadi takardunsu na fita daga ƙasar, ta yadda idan sun je iyaƙar Aswan ta Masar ba za a sha wuyar tantance su ba.

Tun da fari sanarwar ta ambato cewa an kwaso mutum 637 daga Khartoum cikin motoci 13, waɗanda ta ce a halin da ake ciki suke kan iyakar Masar ana tantance su.

Gabanin wannan sanarwa, hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya ta ce daga safiyar Juma’a ne za a fara kwaso ɗaliban ƙasar da ke karatu a Sudan bayan sun isa Aswan a cikin ƙasar Masar.

Kuma jirgin saman Air Peace da zai yi aikin kwashe ɗaliban da sauran ‘yan Najeriya, zai tashi da ƙarfe 6 na yamma zuwa Aswan, cewar shugaban hukumar ba da agajin gaggawar.

To sai dai har yanzu ba a ji ɗuriyar jirgin ba, abin da ya sanya iyaye da sauran al’ummar ƙasar cikin damuwa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Ƴan Bindiga Sun yi wa Tawagar Ƴan Sanda Kwanton Ɓauna a Zamfara, Sun Kashe 5, Sun Sace WasuƳan Ta'adda Sun Mamaye Gona, Sun Sace Ɗaliban Islamiyya 14 a Jihar NejaGombe: PDP ta Kori Mailantarki da Garry Kan Zargin Aikata Ayyukan Cin Zarafin Jam'iyyarHukumar Kwastam ta Tura Bayanan Sirri Masu Amfani da Fasahar AI Don Yaƙi da Labarai na Karya da Zamba ta IntanetSojoji Sun Kai Farmaki Sansanin Masu Sace Mutane a Kogi, Sun Kwace Harsasai 1,000, Babura ShidaMelaye Ya Kalubalanci Tinubu Zuwa Gasar Karatun Alqur'ani Bayan UmrahZaɓen 2027: Ƴan Sandan Najeriya da Birtaniya Sun Horas da Jami'ai 55 Don Haɓaka Ayyukan Yaƙi da Ta'addanciICPC ta Gargaɗi Jami'o'i da Kwalejojin Fasaha Kan Cin Hanci da Rashawa a Ayyukan TETFundGwamnatin Tarayya ta Sauya Dokar Kashe Gobara ta 1963 Zuwa Sabuwar Dokar CetoSojojin Ruwa da na Ƙasa Sun Kashe Ƴan Ta'adda 34 a Sabon Hari a Tafkin ChadiHukumar FRSC ta Kaddamar da Samame a Faɗin Ƙasa Kan Lambar Mota na BogiJama'ar Jigawa na Rera Taken "Dole Tinubu ya Tsaya" Yayin da Shugaban NITDA ke Jagorantar GangaminSanata Buba ya Kai Ta'aziyya ga Masarautar Misau Kan Waɗanda Suka Samu Hadari, Ya Kaddamar da Ofishin Yaƙin Neman Zaɓen Jam'iyyar PRPFBI ta Yabi Najeriya Kan Yakar Cin Zarafin Yara, Tinubu ya Yabawa Hukumar EFCCIGP Disu ya Samu Haɗin Kan Amurka da Italiya Don Horar da Ƴan Sanda 5000
X whatsapp