Home General Kwamandan MNJTF ya mika Motocin yaki ga Dakarun dake Kirawa

Kwamandan MNJTF ya mika Motocin yaki ga Dakarun dake Kirawa

Kwamandan MNJTF ya mika Motocin yaki ga Dakarun dake Kirawa.
Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da shugaban sashen yada labarai na rundunar a N’Djamena dake Chadi laftanal Kanal KAMARUDEEN ADEGOKE, mai dauke da kwanan watan 15 ga watan Disambar 2022.
Sanarwar tace kwamandan rundunar hadin Gwiwar ta MNJTF, Manjo Janar Abdul Khalifa Ibrahim daya sami rakiyar mataimakin sa Birgediya Janal Assouala Blama da kwamandan sashe na 1 na rundunar a kamaru kanal Tiokap Loti yayin ziyarar ta aiki Da suka kai Shalkwatar Rundunar sojin a kirawa dake iyakar Nijeriya da Kamaru a yankin jihar Borno dake Nijeriya a ranar laraba.
Sun sami tarbar Babban kwamandan runduna ta bakwai 7 (GOC) Manjo Janar W Shaibu, bayan bikin tarbar soji ta Al’ada manjo Janar Sha’aibu ya yaba bisa Motocin yaki da aka bawa rundunar kirar ( Toyota Buffalo Hillux fitted for Combat).
Ya yaba ga shugaban Rundunar Sojin Nijeriya Janar Lucky Irabor da shugaban sojin kasa Laftanal Janal F. Yahaya da suka samar da motocin domin inganta ayyukan rundunar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp