An gabatar da kudirin samar da sabuwar jihar Tiga a zauren majalisar Dattijan Nijeriya, wannan na zuwa ne bayan Majalisar Dattawa ta karbi kudirin kafa Jihar Anioma a yankin Kudu maso Gabas, wanda Sanata Ned Nwoko daga Delta ta Arewa ya gabatar.
Kudurin dokar wanda Sanatan Kano ta kudu Suleiman Abdurrahman Kawu Sumaila ya gabatar, wanda aka yi masa karatu na farko a ranar 10 ga Yuli, 2024.
Kudirin dokar mai taken “Constitution of the Federal Republic of Nigeria, 1999 (Alteration) Creation of Tiga State Bill, 2024 (SB.523)” na da nufin raba jihar Kano zuwa jihohi biyu, inda Tiga za ta zama sabuwar jihar da za a kirkireta daga jihar kano.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Bugu da kari, an gabatar da kudirin dokar kafa jihar Orlu, wanda Sanata Osita Izunaso da mai wakiltar Ikenga Ugochineyere, da kuma jihar Etiti suka gabatar, wanda dan majalisa Amobi Godwin Ogah da wasu ‘yan majalisa hudu daga al’ummomin da abin ya shafa suka dauki nauyinsa.
Akwai kuma kiraye-kirayen a kirkiro sabbin jihohi daga Legas da sauran sassan kasar nan.
jihar Kano dai na guda cikin jihohin dake Arewa maso yammacin Nijeriya dake da tarin Alúmma, wanda ake kallon hakan taka muhimmiyar rawa wajen dakile cigaban Alummar ta.
PRNigeria Hausa











