Home DUNIYA An kama mai garkuwa da mutane a wajen karbar kudin fansa a Yobe

An kama mai garkuwa da mutane a wajen karbar kudin fansa a Yobe

Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe dake arewa maso gabashin Nijeriya ta tabbatar da kama Usman Garba mai kimanin shekaru 30 da take zargi da ayyukan garkuwa da mutane a jihar.

Kakakin rundunar, DSP Dungus Abdulkarim ne ya bayyana hakan, inda yace a ranar 5 ga watan Yunin shekarar 2024 da misalin karfe 1 na yamma, jami’ai daga sashen (SID) suka sami nasarar kama Usman Garba dan Asalin kauyen Katarko dake karamar hukumar Gujba, a kan hanyar sa ta zuwa kashe kason da ya samu a wata garkuwa da suka gudanar.

”Wanda ake zargin guda ne cikin mabobin wata tawaga da suka kware wajen fashi  da makami, garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da kuma satar shanu a karamar hukumar hukumar Gujba da garuruwan dake makotaka da garin.

”Tawagar suke da alhakin garkuwar da akayi baya-bayannan a wani wurin zaman fulani da ake kira da Babaram Muktum a karamar hukumar ta Gujba, inda suka yi garkuwa tare da karbar kudin fansa naira miliyan 1 da dubu dari 6.

“sauran mambobin kungiyar sun tsere, amma rundunar na kokari domin tabbatar da ta kamasu.”

PRNigeria hausa

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp