NAWOJ ta taya Al’ummar Nijeriya Murnan Mauludin Annabi Muhammad S.A.W

Kungiyar mata ‘yan jaridu reshen Kano NAWOJ ta ta bukaci daukacin al’ummar musulmi Nijeriya da su yi koyi da kyawawan halaye na fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (S.A.W).

Wannan dai na cikin wata takardar manema labarai da kungiyar ta fitar, mai dauke da sa hannun sakatariyar kungiyar Maryam Muhammad a wani bangare na bikin murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammadu S.A.W.

Sanarwar ta ambaci shugabar kungiyar Kwamared Bahijja Kabara na kira ga mata ‘yan jaridu da su rubanya kokarinsu ta hanyar bin koyarwar Annabi S A W wajen biyayya ga mazajensu da kuma kyautata alaka da makwabta.

Kwamaret Bahijja ta kuma yi kira ga mata da su koya wa ‘ya’yansu tarihin Annabi Muhammadu ​​tare da yin koyi da halayensa domin kyautata rayuwar al’umma.

Hakazalika Kwamared Bahijja Kabara ya yi kira ga masu hannu da shuni da su taimaka wa marasa galihu kamar yadda aka koya daga koyarwar Annabi Muhd. S.A.W

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 4 hours 35 minutes 31 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 6 hours 16 minutes 56 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com