Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi wa ma’aikatu da wasu hukumomin gwamnatin Najeriya garambawul, inda aka haɗe wasu aka kuma ƙirƙiru wasu.
Wata sanarwa da mai magana da yawun fadar shugaban ya fitar ta ce Tinubu ya ba da umarnin rusa hukumar bunƙasa yankin Neja-Delta da kuma ma’aikatar wasanni.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Bayo Onanuga ya ce a madadin haka, yanzu za a ƙirƙiri ma’aikatar bunƙasa yankuna da za ta kula da hukumomin yankunan da ake da su.
Sai kuma hukumar kula da wasanni ta ƙasa da za ta maye gurbin ma’aikatar wasanni.
Haka nan, majalisar zartarwa ta amince da haɗe ma’aikatar al’adu da ma’aikatar yawon buɗe ido wuri guda.











