‘Yan bindiga dake jihar Niger a tsakiyar Nijeriya sun yi awon gaba da mutane a 20 a cikin motoci 5 da suka tare a hanyar Mariga-Kontagora.
kakakin majalisar jihar Niger, dan majalisa mai wakiltar mazabar mariga Barister Abdulmalik Sarkin-Daji ne ya tabbatar da hakan yayin da yake ganawa da manema labarai.
yace labarin ya faru ne a ranar alhamis yayin da ‘yan bindigar suka tare hanyar Mariga-kontagora tsakanin Babban-Lamba da Beri.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
wannan dai jawabi na kakakin majalisar na matsayin martani ga rundunar sojojin Nijeriya, wadda ta musanta cewa ‘yan ta’addan basu mamaye wajen horar da dakarunta dake karamar hukumar Kontagora ba wanda yanzu haka sun fafadada zuwa karamar hukumar Mariga.
sarkin daji yace iyalen wadanda aka yi garkuwa da su, sun sha kai kudin fansa ga ‘yan ta’addan, wanda kuma wajen horar da dakarun sojojin Najeriya ne wajen da ake kai kudin fansar.
yace wadanda aka sako din sun bayyanawa iyalen su cewa, an ajje su ne a dajin da babub nesa da barikin sojoji ta Kontagora.
haka kuma ya kara da cewa Fasinjojin da ‘yan ta’addan suka kama ranar alhamis sun kai su ne zuwa wannan daji, in da ya bukaci dakarun sojojin sun sami bayani na gaskiya domin su fitar da ‘yan bindigar daga cikin daji.











