Home General Gwamnatin jihar Kano ta Amince da kashe sama da biliyan 8 domin...

Gwamnatin jihar Kano ta Amince da kashe sama da biliyan 8 domin manyan ayyuka 15

Majalisar zartaswar jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta amince da kashe Naira 8,199,635,732.07 domin gudanar da manyan ayyuka 15 a fadin jihar.

Wannan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar bayan tattaunawa a taron majalisar zartarwa karo na 24 da aka gudanar a gidan gwamnatin Kano ranar Laraba.

An ware naira 2,737,518,204.96 domin gina ajin karatu mai ajujuwa huɗu a fadin kananan hukumomin jihar 44.

Haka kuma majalisar ta amince da fitar da naira 2,311,388,177.70 domin sake aikin gina titin shataletalen gidan gwamnati zuwa titin Lodge Road, zuwa Race Course zuwa shataletalen otal ɗin Daula, tare da ƙarin ayyukan da suka shafi titin asibitin Nasarawa, titin Dawaki da kuma titin Lugard.

An ware Naira 1,870,814,360.10 domin gyaran babban ɗakin taro na Africa House da ayyukan tuntuɓa a gidan gwamnati.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp