Home General Najeriya da China sun cimma yarjejeniyar Yuro biliyan 7 a bangaren makamashi

Najeriya da China sun cimma yarjejeniyar Yuro biliyan 7 a bangaren makamashi

Najeriya da China sun rattaba hannu akan yarjejeniyar samar da makamashi mara gurɓata muhalli da ya kai Yuro biliyan 7 da miliyan ɗari 6 da zummar sauyawa daga amfani da makamashi mai gurɓata muhalli daidai da yadda dokokin duniya suka tanada.

A ƙarshen makon da ya gabata ne aka tabbatar da wannan yarjejeniya a hukumance a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom a  tsakanin gwamnatin Najeriya da kamfanin  APPL Hydrogen Limited (AHL), da LONGi Green Energy Technology Company Limited  na ƙasar China.

Za a gudanar da wannan aiki ne yankin da aka sakar wa yan kasuwa mara su gudanar da sabgoginsu, wato Liberty Free Trade Zone da ke garin Atabrikang a ƙaraamar hukumar  Ibeno ta jihar Akwa Ibom.

Kamfanin LONGi, wanda ke kan gaba a hakar sauyawa zuwa amfani da makamashi mara gurɓata muhalli a duniya, da AHL na Najeriya, wanda ya ƙware wajen samar da makamashi da ba ya illata muhalli ne za su yi haɗaka don tafiyar da aikin, kamar yadda yake a cikin yarjejeniyar fahimtar juna da aka yi.

Da yake jawabi a yayin rattaba  hannu a yarjejeniyar, ministan kimiyya da fasaha na Najeriya, Uche Nnaji ya jaddada mahimmancin shirin a koƙarin da Najeriya ke yi wajen sauyawa zuwa amgfani da makamashin da ba ya illa ga muhalli.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Shin AtikuObi Zasu Iya Tsige TinubuShettima a 2027? Daga Yushau A. ShuaibYadda Shari'ar Masarautar Kano ke Ci gaba da Wakana a Kotun ta ƙoliTawagar Amurka na Shirin Tafiya Pakistan Domin Tattaunawar Sulhu da IranDole Najeriya ta Samu Tsaro ta Kowane Hali - Babban Hafsan TsaroChelsea da Newcastle na Harin Coulibaly, Liverpool na Neman Siyan Marcos SensiBadaƙalar $1.3m: Kotu ta ba EFCC izinin Kama Tsohuwar Ministar jin ƙan Najeriya Sadiya FarouqRaphinha ya Magantu kan Fitar da ƙungiyarsa da aka yi Daga Champion LigRundunar sojin Najeriya ta Musanta bai wa Tsofaffin Mayaƙan Boko Haram MakamaiGwamnatin Tarayya ta Sauya Zarge-Zargen da ta ke yi wa MalamiAn Binne Birgediya Janar Braimah da Sauran Sojojin da Boko Haram ta KasheYaƙin Iran: Hauhawar farashin Kaya a Najeriya ya ƙaruAdadin Matasa 'Yan kwaya da Muka Kama a Shekara 5 - NDLEAJam'iyyar ADC ta Kori Nafi'u Bala GombeRigakafin ƙyanda ya Ceci Yara Miliyan 20 a Afirka - Hukumar Lafiya ta Duniya2027 Ita ce Dama ta ƙarshe da zan Fito Takara - Atiku
X whatsapp