Home SIYASA Bai Dace Obasanjo ya Danganta Marigayi Ghali Na’abba da Zargin Cin Hanci...

Bai Dace Obasanjo ya Danganta Marigayi Ghali Na’abba da Zargin Cin Hanci ba – Atiku

Bai Dace Obasanjo ya Danganta Marigayi Ghali Na’abba da Zargin Cin Hanci ba – Atiku

 

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya yi watsi da sabon zargin da tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo ya yi masa, yana mai cewa ƙoƙari ne na ɓata masa suna domin ba wa ɗan takarar da yake goyon baya gabanin zaɓen 2027.

A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu ya fitar Atiku ya ce bai dace Obasanjo ya danganta marigayi tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Ghali Umar Na’Abba da zargin cin hanci ba, alhali ba ya raye don ya kare kansa.

Ya kuma ce, idan har akwai hujjar aikata laifin kamar yadda aka yi zargin ya kamata gwamnatin Obasanjo ta ɗauki mataki tun lokacin da lamarin ya faru.

Atiku ya yi zargin cewa, lokacin da aka sake tayar da batun na da alaƙa da shirye-shiryen siyasar zaben 2027, yana mai cewa tsohon shugaban ƙasar ya kamata ya fito fili ya bayyana ɗan takarar da yake goyon baya maimakon amfani da tsofaffin zarge-zarge wajen janyo ra’ayin jama’a.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Ƴan Sandan Legas Sun Kama Mutum 4 da Ake Zargi da Fashin Daji, Sun Kwato Wayoyin Hannu 25, Kwamfutoci da Kayan Ado na ZinareRundunar Sojin Ruwa Ta Rusa Wuraren Tace Mai Ba bisa Ka’ida Ba, Ta Kwato Lita 350 na AGO a Rivers2027: Yahaya Bello Ya Tara Masu Daidaita Ayyuka na A4A a Arewa ta Tsakiya Domin sake Zaban TinubuSojoji Sun Kama Mutum 2 da ake Zargi da Taimakawa Ƴan Ta’adda, Sun Kwace Kayayyakin Babur a YobePDP Ta Yi Gargadi Kan Zargin Tattara Katunan Zabe PVC da Bayanan Asusun Banki a GombeRundunar Sojojin Najeriya ta Sauya Manyan Janarori Zuwa Muhimman Mukamai na Aiki da DabaruHukumar INEC za ta ƙaddamar da Na’urar Bibiyar shirye-shiryen Zaɓen 2027 kai TsayeDaliban Tallafin Horarwa na Prnigeria Sun Ziyarci Emirate FM, Sun Samu Kyawawan Bayani Kan Watsa Labarai na DijitalNSCIA ta yi Allah Wadai da Nuna Bambancin Addini a Ci gaba da Tsare El-RufaiSarkin Ilorin Ya Yaba da Tallafin Horarwa na PRNigeria Wajen Shirya Masu Watsa Labarai na Nan GabaNDLEA Ta Kama Mai Safarar Hodar Iblis da ake Zargi da Laifi Akan Jigilar Kaya a Saudiyya, ta Kuma Kama Kwayoyi Masu Yaduwa Sama Da Miliyan 2Gwamnatin Tarayya ta Yaba da N5.41 Trillion da Kwastam ta Tara, Ta Nemi a bi Ka'idojin Duniya Hukumar Kwastam Ta Naɗa DCG, ACG 5, ta yi Nazarin Yadda aka Samu Kuɗin Shiga2027: HURIWA Ta Bukaci Ƴan Sanda da su Gurfanar da Ƴan Siyasa Kan Zargin Kalamai Masu Tada HankaliSojoji Sun Tarwatsa Maboyar Ƴan Ta'adda, Sun Kwace Bindigogin AK-47 a Sokoto 
X whatsapp