Home SIYASA Zaɓen 2027: Uba Sani ya zaɓi Mataimakinsa

Zaɓen 2027: Uba Sani ya zaɓi Mataimakinsa

Zaɓen 2027: Uba Sani ya zaɓi Mataimakinsa

 

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya sanar da zaɓen mista Jerry Adams a matsayin mataimakinsa a zaɓen gwamnan 2027, bayan shawarwari da addu’o’i da ya ce sun jagoranci wannan mataki.

A cikin wata sanarwa da gwamnan ya fitar a shafinsa na X, Uba Sani ya ce zaɓar Adams ya yi daidai da manufar gwamnatinsa ta haɗin kai, adalci da bai wa kowane ɗan jihar damar jin yana da muhimmanci a harkokin gwamnati, ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba.

Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi ƙoƙarin tabbatar da ci gaba a dukkan ƙananan hukumomin jihar tare da ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai tsakanin al’ummomi.

Gwamnan ya yaba wa Jerry Adams a matsayin gogaggen jami’in gwamnati kuma ƙwararren mai kula da harkokin haraji, yana mai cewa mutumin ne mai gaskiya, ƙwazo da kishin zaman lafiya, wanda zai taimaka wajen ci gaba da gina Kaduna mai haɗin kai da ci gaba.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 15 Sun Mutu a Sabon Harin Yan Bindiga a Jihar Benue Zaɓen 2027: Uba Sani ya zaɓi MataimakinsaJami'an Tsaro Sun Kuɓutar da Mutane 32 Yayin da 4 Suka Mutu a Jihar Sokoto China ba za ta Bayar ko ta Sayar wa Iran Makamai ba a Kowane h Hali - TrumpBai Dace Obasanjo ya Danganta Marigayi Ghali Na'abba da Zargin Cin Hanci ba - AtikuGarkuwa da Mutane: Dakarun Sojin Najeriya Sun Kama Mutane 5 a Jihar Yobe Sojojin Najeriya na Neman ɗaya Daga Cikin Jami'inta Ruwa a Jallo, Kan Zargin Sayar wa Ƴan bindiga Kakin SojiYaɗa Farfaganda da ƙiyayya Kan Gwamnati ba Zai Kawo ƙarshenta ba - MatawalleMawallafin PRNigeria Ya Fitar Da Littafin Tarihin Rayuwarsa Akan Rigimar NIPSS Yayin Da IMPR Ta Bayyana Cigaba Mai Karfi A Tsakiyar ShekaraShugaban Amurka ya Yaba wa Shugaba Tinubu Kan Matakan da Yake ɗauka Wajen Yaƙi da Ta'addanciBinciken Gaskiya: Shin Gajimaren ne ya ɓulɓulowa ƙasa a Hanyar Abuja Zuwa Kaduna?HRW ta Zargin Hukumomin Najeriya da Rashin Adalci ga Ƴan  ƙungiyar Boko HaramHukuncin da Kotu ta Yanke wa Matashin da ya  Yunƙurin Satar Motar Yan SandaMutane 6 Sun Rasu 4 Sun Jilkata Sanadiyyar Tsawa a Jihar AdamawaMatatar Dangote ta Dakatar da Amfani da Naira Wajen Sayar da Man Fetur
X whatsapp