Home General Bincike: Akalla Masu Fama Da Ciwon Koda 230 Ke Fuskanta Hadari Dukkan...

Bincike: Akalla Masu Fama Da Ciwon Koda 230 Ke Fuskanta Hadari Dukkan Mako Sakamakon Karancin Injinan Wankin Kodar A Jihar Kano.

Masu fama da ciwon Koda a jihar Kano dake Arewacin Nijeriya na kara shiga cikin hadari sakamakon rashin isassun injinan wankin kodar domin kula da masu fama da ciwon, inji rahoton bincike da PRNigeria ta gudanar.

Wani bincike da PRNigeri ta gudanr a baya-bayannan ya tabbatar da cewa cutar Koda (CKD) na ci gaba da karuwa a jihar Kano, ya kuma nuna cewa sama da majinyatan dake fama da cutar 200 a jihar sun dogara ne da injinan wankin kodar guda 12 kacal a manyan Asibitocin jihar da suka hadar da Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH), da Asibitin kwararru na Abdullahi Wase.

Binciken ya nuna cewa, akalla majinyata 160 da ke fama da ciwon kodar ke ziyartar asibitin kwararru na Abdullahi wase duk mako. Har ila yau, akwai sabbin majinyata 15 da ke zuwa don yin wankin koda ko wanne mako.

A yayin da a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano inda ake samun majinyata kusan 70 dake bukatar wankin kodar, Amma a cikin makon akalla mutum 40 kan jira domin yi musu wankin.

Duk da tsadar da magungunnan da masu fama da wannan lalura ke da shi, PRNigeria ta bankado cewa da yawa daga cikin Na’ororin wankin kodar a manyan cibiyoyin lura da masu fama da lalurar guda 2 dake jihar Kano basa aiki.

Bincike na PRNigeria ya kuma nuna cewa a Asibitin koyarwa na Aminu Kano, injinin wankin kodar guda 8 ne kawai ke aiki a halin yanzu, kuma da yawa daga cikin masu fama da cutar suna jiran sama da sa’oi 10 kafin a yi musu wankin.

Aliyu Abdullahi, Farfesa a fannin likitancin Kodar dake jami’ar Bayero a jihar Kano, haka kuma shugaban sashin kula da cutar na Asibitin koyarwa na  Aminu Kano, ya ce abu ne mai matukar wahalar gaske a iya jure aiki da injinan wankin kodar da majinya da dama ke zaman jira domin ayi musu magani.

“A da muna da injinan wankin kodar har guda 20, amma saboda rashin isassun kudade da sauran kalubalen da muke fuskanta a halin yanzu bamu da injina sama da 5 da ake aikin da su.

“Yana da matukar wahala a iya jurewa. Za ku ga marasa lafiya suna yin layin na awannin 10 ko 15 don samun wankin Kodar saboda lokacin da kuka sanya majinyaci a kan injin wanki, dole ne ya zauna na akalla sa’oi 4, sannan kuma kuna bukatar Karin sa’a 1 don tsaftacewa da kashe kwayoyin cutar daga kan injin kafin a shirya don majinyaci na gaba. Don haka zaku iya gani a rana daya, ba za ku iya dora marasa lafiya sama da guda 3 a kan na’ura guda ba.”

A  Asibitin kwararru na Abdullahi Wase, wanda ake kallo matsayin asibitin mafi arahar cibiyar lura da masu fama da lalurar kodar a Kano, hudu (4) ne kadai daga cikin injina shidan (6) da ake dasu ke aiki.

PRNigeria ta tattaro cewa ana gudanar da duk maganin kodar cikin farashi mai sauki sakamakon, tallafin da Gwamnatin jihar ke bayarwa, amma duk da haka, ana kara ganin adadin masu fama da wannan lalura dake jiran wankin na karuwa a sashen.

Mukaddashin shugaban sashen masu fama da cutar Koda a Asibitin kwararru na Abdullahi Wase, Dakta Usman Adamu, Yace maganin cutar nada araha sosai domin farko naira dubu 15,000 ake saya sannan kuma naira dubu 8,000, kowannensu yana da araha idan aka kwatanta da sauran cibiyoyi.

“A nan muna da injinan wankin kodar kusan guda hudu, ana gab da gyara guda biyu. Hakazalika, a wannan asibiti muna samun matsakaicin adadin marasa lafiya 60 zuwa 80 a kowanne asibitin da kuma masu fama da cututtukan dake da alaka da koda, kuma daga cikinsu akwai da dama dake  bukatar wankin kodar, sannan akalla akan sami sabbin majinyata 15 da ke zuwa domin yin wanki a wanna asibiti”.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HURIWA ta Soki Ƴan Sanda da NDPC Kan Jinkirin Binciken Zargin Kutse da aka yi wa Bayanan NIPSS da ya Shafi Jami’in Sojan RuwaƳa'yan El-Rufai Sun Shiga Rikici Yayin da Bashir ya Zargi Bello da Shan Muggan Kwayoyi da Cin Amanar suTsaro, Fafutuka da Nauyin Tabbatarwa Daga Mukhtar Ya’u MadobiONSA ta Fitar da Faɗakarwar Tsaro, ta Bukaci Ƴan Najeriya su ƙara Yawan Tsawaita TsaroHukumar DSS ta Dakatar da Shari'ar Sowore Kan Laifukan Intanet Har Sai Bayan Zaben Shugaban Kasa na 2027Gwarzo ya ba da Gudummuwar ₦10m ga Horarwa na Musamman na PRNigeria Bayan ya ba da Gidansa na Abuja Don Cibiyar Koyon Aikin Jarida2027: Bayan Takardu da Sauran Tsoffin Maganganu Marasa Amfani, ‘Yan Najeriya Sun Cancanci Kamfen Din da Ya Dace Da Matsaloli  Daga Kabir AkintayoGwamnati Tarayya ta Bayyana Bas 100 Masu Amfani da Wutar Lantarki Don Rage Wa Ma’aikatan Gwamnati Matsalar SufuriƳan Ta’adda na Amfani da Kafafen Sada Zumunta da Dandamalin Aikin Tura Kuɗi Don Tallafa Wa Ayyukansu — BukartiBinciken Gaskiya na PRNigeria: Ta Karyata Da’awar Tony Elumelu ta Cewa An yi Satar Man Fetur Kashi 97% Kafin Zamanin TinubuMeyasa Mutuwar Bazata Take Daukar Masu Alheri ta Bar Mugaye ? Na Yushau A. ShuaibSojoji Sun Kama Bindigar AK-103 Da Aka Boye a Cikin Jakar Gero, Sun Kama Mutum Uku A ZamfaraSojoji Sun Kama Shahararren Shugaban Ƴan Bindiga, 'Sanusi Maigilas' a Dajin Katsina2027: Yadda Zan Magance Rashin Tsaro, In Magance Matsalolin Tattalin Arziki da Zamantakewa a Kwara — Zakari MohammedLabarin NIPSS Mai Damuwa: Lokacin da Jami'in Sojan Ruwa Ya Cin Zarafin Mawallafi Daga Nuhu Mohammed
X whatsapp