Gwamnan jihar Kano Abba kabir Yusuf ya sanya hannu kan dokar Masarautar Kano ta shekarar 2024.
Ta cikin jawabin Gwamnan ya ayyana Muhammadu sunusi II a matsayin sabon sarkin Kano na 16.
Haka kuma ya bawa sarakunan da dokar majalisar ta rushe wasu sa’oi da su gaggauta ficewa daga masarautun nasu.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Tun da fari dai Majalisar dokoki ta jihar Kano ta amince da rushe duka masarautun jihar bayan soke sabuwar dokar da ta ƙirƙiri sababbin masarautu a 2019.
Hakan na nufin cewa an koma amfani da tsohuwar dokar da ta kafa masarautar Kano.
Majalisar ta ɗauki matakin ne a zaman da ta yi ranar Alhamis.
Sabon matakin da majalisar ta ɗauka ya nuna cewar sarakunan jihar biyar na Kano, da Bichi, da Ƙaraye, da Gaya, da Rano duk sun rasa kujerunsu.
PRNigeria Hausa












