Babu batun ‘yancin Madigo, Luwadi, Bisexual, Transgender da Queer (LGBTQ) – Samoa

Kungiyar Lauyoyin Nijeriya ta NBA ta ce a cikin yarjejeniyar Samoa babu wani abu da ya tilastawa Najeriya amincewa da ‘yancin ‘yan Madigo, Luwadi, Bisexual, Transgender da Queer (LGBTQ).

Shugaban kungiyar Mista Yakubu Maikyau (SAN), ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yadda labaran Kungiyar NBA na kasa, Mista Habeeb Lawal, Maikyau ya yi gargadi game da munanan labaran da ke tasowa daga bayanan karya kan yarjejeniyar.

Ya ce: “ Hankalina ya karkata ga yadda ake buga jaridu da kafafen sada zumunta na zamani, game da martanin da wasu ‘yan Najeriya suka yi, game da rattaba hannu kan yarjejeniyar SAMOA da gwamnatin tarayya ta yi.

 

“Sabanin labarin da ake yadawa ko dai saboda rashin sanin abin da yarjejeniyar ta kunsa ko kuma da gangan na yaudarar jama’a,.

“Wannan babu wani tanadi a cikin yarjejeniyar Samoa da ta bukaci Najeriya ta amince ko ta kowace hanya ta amince da LGBTQ ko ‘yan luwadi, ko dai a matsayin wani sharadi na bashi dala biliyan 150 ko kwata-kwata.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 9 hours 42 minutes 40 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 11 hours 24 minutes 5 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com