Majalisar Wakilan Nijeriya ta bukaci gwamnatin Tarayya ta yi gaggawar dakatar da yarjejeniyar SAMOA da ta haifar da cece-kuce da zargin taba martabar addini da al’adun mutanen Nijeriya.
Majalisar ta kuma yanke shawarar bincikar yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta rattabawa hannu a ranar 28 ga watan Yuni.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
An zartar da kudurin ne biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa na Ali Sani Madaki, sashin marasa rinjaye, da wasu ‘yan majalisa 87 suka dauki nauyi.
Kwanan nan yarjejeniyar ta haifar da cece-kuce saboda rahotannin cewa an shigar da tanade-tanade da suka shafi ‘yan madigo, ‘yan luwadi, bisexual, da transgender (LGBT) a cikin yarjejeniyar.
sai dai wannan na zuwa ne daidai lokacin da kungiyar lauyoyin kasar ta NBA da ake kallon matsayin masana doka suka fitar da sanarwar dake cewa cikin yarjejeniyar babu wani batun auren jinsi ko makamantan sa.
PRNigeria hausa











