Jami’ar Jihar Kwara ta kori dalibai 175 bisa gudanar karya doka da laifukan da suka shafi satar Jarrabawa a jami’ar.
wannan dai na cikin wata sanarwa da mukaddashin daraktan yada labarai da hulda da jama’a ta jami’ar Dr. Saeedat Aliyu ta fitar wadda aka raba manema labarai a ranar litinin.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
sanarwa ta ce daliban da jami’ar ta kora na cikin wadanda aka samu da laifukan da suka shafi satar jarrabawa, sata, amfani da sakamakon Bogi domin samin damar fara karatu a Jami’ar, tayar da tarzoma, damfara, shiga cikin haramtattun kungiyoyi da sauransu.
sanarwa ta ce wadannan sune dalilan da suka sa hukumar gudanarwa Jami’ar korar daliban duba da karya kaída da dokokin ta.
PRNigeria Hausa











