Gwamnatin tarayya kasar nan tace zata kashe naira tiriliyan 3 wajen biyan mafi karancin albashi da kuma biyan fansho da garatitun ma’aikatan kasar nan.
Ministan kasafi da tsare tsare Atiku Bagudu ne ya bayyana hakan, yayinda yake ganawa da mambobin kwamitin majalisar dattijai kan kasafi wanda olamilekan Adola ke jagoranta.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
A yayin ganawa Ministan ya gabatar musu ga daftarin sabon kudirin mafi karancin albashin na shekarar 2024.
Idan dai za’a iya tunawa shugaban kasa Bola Tinubu, ya amince da biyan naira dubu 70 matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan kasar nan bayan wata ganawa da yayi da shugabancin kungyoyin kwadago na NLC da TUC
Haka kuma shugaban kasar ya bukaci yin nazari kan dokar albashin dukkanin bayan shekaru uku a madadin shekaru biyar da ake dubawa a baya.
PRNigeria hausa











