Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta jihar Ebonyi, EBSIEC, ta bayyana jam’iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zaben kananan hukumomin jihar da ya gudana a ranar Asabar
Shugaban Hukumar Jossey Eze ya bayyana hakan a Abakaliki, inda ya ce jam’iyyar ta lashe dukkan kujerun Shugabancin Kananan hukumomi 13 da Kansiloli 171da ke jihar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Eze ya ce jam’iyyun siyasa uku ne Suka shiga zaben, Wanda suka hada da jamiyyar APC, APGA da Kuma Labour Party.
Tuni dai shugaban hukumar zaben ya sanar da amincewar sakamakon.
Daga nan sai ya yabawa masu ruwa da tsakin na hukumar, da Kuma jami’an tsaro Kan yadda aka Sami nasarar gudanar da zaben lafiya.
PRNigeria Hausa











