Home General Tinubu ya rantsar da Kudirat Kekere-Ekun babbar mai shari’a ta Najeriya

Tinubu ya rantsar da Kudirat Kekere-Ekun babbar mai shari’a ta Najeriya

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya rantsar da Mai Shari’a Kudirat Olatokunbo Kekere-Ekun domin kama aiki a matsayin babbar mai shari’a ta ƙasa a ranar Litinin bayan Majalisar Dattawa ta amince da naɗin nata.

Ita ce mace ta biyu da take riƙe muƙamin a tarihi, kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa ta bayyana.

An yi bikin rantsuwar ne a gaban tsofaffin manyan alƙalai huɗu, ciki har da mace ta farko da ta riƙe muƙamin Mariam Aloma Mukhtar.

“Fannin shari’a babban ginshiƙi ne da ke tallafe da tsarin dimokuɗaiyarmu, kuma tsawon shekaru fannin shari’ar Najeriya ya sha nuna tasirinsa na mai shiga tsakani domin tabbatar kowa ya bi doka,” a cewar Shugaba Tinubu yayin taron.

“Matsayinki na zama wuri na ƙarshe da talaka zai samu adalci yana da muhimmanci wajen saka wa mutane ƙwarin gwiwa kan dimokuraɗiyya,” in ji shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba Hatsarin Jirgin Sama na Ondo: Disu Ya Jajantawa NAF, Ya Jaddada Goyon Bayan Ƴan Sanda
X whatsapp