Home General EFCC ta kama tsohon gwamnan Taraba kan badakalar Biliyan 27

EFCC ta kama tsohon gwamnan Taraba kan badakalar Biliyan 27

Hukumar dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa ta EFCC ta tsare tsohon Gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku bisa zargin halasta kudin haram ya zuka kai naira biliyan 27 a lokacin da yake bisa karagar mulkin jihar

EFCC ta na tuhuwar tsohon Gwamnan  wasu tuhume-tuhume guda goma sha biyar dake da nasaba da almundahana da dukiyar al’umma

Rahotanni sun bayyana cewa, a wannan Juma’a ne jami’an EFCC suka yi dirar mikiya a gidan tsohon gwamnan da ke Abuja wanda wa’adinsa ya ƙare a shekarar 2023 bayan shafe tsawon shekaru takwas a kan madafun iko.

EFCC ta ce gwamnan yana hannun hukumar inda ake titsiye shi.

Hukumar ta EFCC ta kammala tattara aƙalla tuhume-tuhume 15 da ake zargin tsohon gwamnan kuma nan ba da jimawa ba zai gurfana a gaban kuliya.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp