Sojojin Nijeriya sun Jajjada biyayyarsu ga Tinubu

Hedikwatar tsaron Najeriya ta gargaɗi ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi da ke kira ga sojoji su yi juyin mulki a ƙasar, tare da jaddada cewa yin hakan cin amanar ƙasa ne a ƙarƙashin kundin tsarin mulki.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da darektan yada labarai na hedikwatar tsaron, Birgediya Janar Tukur Gusau ya fitar, inda ya ce sojojin za su ci gaba da mayar da hankali a kan babban aikin da ya wajaba a kansu, wanda ya haɗa da kare yankin ƙasar tare da tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Hukumomin sojin sun kuma ƙara jaddada biyayyarsu ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da ƙudurinsu na kare tsarin dumukuraɗiyya a ƙasar.

Darektan ya ƙara da cewa ya kamata masu neman sojoji su yi juyin mulki, kamar yadda aka gani a wani hoton bidiyo da ake ta yaɗawa, su sani cewa wannan abu cin amanar ƙasa ne a bisa tanadin kundin tsarin mulki.

Janar Gusau, ya kuma ce zaman lafiyar da aka samu a ƙasar a yanzu, ya samu ne sakamakon goyon bayan da shugaban ƙasar ke ba wa sojoji da kuma jajircewar shugabancin sojojin.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa sojojin tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro za su ɗauki dukkanin matakan da suka dace wajen hana duk wani yunƙuri na sauyin da ta hanyar kundin tsarin mulki ba.

Hedikwatar tsaron ta Najeriya ta fitar da wannan sanarwa ne, bayan da aka riƙa yaɗa wani hoton bidiyo a kwakin nan inda wasu ke kira ga sojoji su yi juyin mulki a Najeriyar.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 14 hours 37 minutes 32 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 18 minutes 57 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com