Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta ɗauki mataki a kan jihohin da suka ƙi gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi da zai tabbatar da cin gashin kai na ƙananan hukumomin kamar yadda kotun ƙolin ta zartar.
Babban lauyin gwamnatin tarayyar Mista Lateef Fagbemi, wanda ya bayyana hakan a jihar Ekiti a jiya Talata, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito ya ce ba gudu ba ja da baya a kan shirin aiwatar da hukuncin kotun ƙolin kan cin gashin ƙananan hukumomin.
Mista Fagbemi ya ce gwamnatin za ta yi nazarin dokokin jihohi a kan zaɓen ƙananan hukumomi tare da duba dalilin da ya sa wasu jihohinke jinkirin gudanar da zaɓen.
Bayanai sun nuna cewa a yanzu sama da ƙananan hukumomi 164 ne a jihohi takwas ba su yi zaben ba.
Jaridar ta kuma ruwaito cewa, wasu rahotanni na nuna cewa wataƙila Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar da hukuncin kotun ƙolin a kan cin gashin kai na ƙananan hukumomi nan da ƙarshen watan nan na Oktoba.
Hakan na nufin gwamnatin tarayyar za ta iya riƙe kason kuɗin ƙananan hukumomin da ba a yi zaɓe ba, kamar yadda hukuncin kotun ya ayyana.
Ƙananan hukumomin da ba a yi zaɓe ba na jihohin Katsina da Zamfara da NasarawaOndo, da Osun da Ogun da Cross Rivers.
Hukuncin kotun ya nuna cewa, saɓa doka ne gwamnonin jihohi su ci gaba da karɓa ko riƙe kason kuɗaɗen ƙananan hukumomi a ƙarƙashin asusun haɗin gwiwa na jida da ƙananan hukumomi.
Wasu gwamnonin jihohin ƙasar dai na ganin wallen hukuncin kotun.
A makon da ya wuce gwamnan jihar Anambra Farfesa Chukuma Soludo, a lokacin sanya hannu kan dokar mulkin ƙananan hukumomi ya yi gargaɗin cewa ba wa ƙananan hukumomin ƙasar 774 cikakken ƴancin cin gashin kai ka iya haifar da abin da ya kira ”gagarumar matsala” ta yarda za a kasa samar da cigaba mai ɗorewa.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 28 minutes 22 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 9 minutes 47 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com