Home General Wasan kwaikwayo ne faduwar da yara 6 da aka kai kotu suka...

Wasan kwaikwayo ne faduwar da yara 6 da aka kai kotu suka yi – IG

Faduwar da yaran da ake zargi da shiga zanga-zanga su ka yi a kotu shiri ne – Babban Sifeton Ƴansanda

Sufeto-Janar na ‘Yansanda, Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa yanke jiki da faduwa da wasu yara shida da ake zargi da zanga-zanga suka yi a kotu kafin gabatar da su a gaban alkali ya kasance wani shiri ne da aka tsara don jan hankalin jama’a ga abin da ba daidai ba.

Egbetokun ya jaddada cewa, duk da haka, an ba da taimakon likita cikin gaggawa, ya na mai bayyana cewa ‘yansanda su na da alhakin kula da lafiyar wadanda suke tsare.

A ranar Juma’a, an gurfanar da mutane 76, yawancinsu kananan yara wadanda ke fama da rashin isasshen abinci, a gaban kotu dangane da zanga-zangar #EndBadGovernance. Goma sha shida daga cikinsu sun fadi kuma aka fitar dasu daga cikin kotun.

Bayan gurfanar da su, kotu ta ba kowanne yaro beli wanda aka sa a kan Naira miliyan goma. Wannan al’amari ya haifar da suka a gida da waje.

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa a wata sanarwa mai kwanan wata Nuwamba 1, da mai magana da yawun rundunar Muyiwa Adejobi ya sanya wa hannu a madadin Sufeto-Janar din, Egbetokun ya tabbatar da cewa, a karkashin dokar Najeriya, wadanda suka kai shekarun aikata laifuka sun isa a hukunta su duk da karancin shekarunsu.

Ya ce, “A yau, wani abu da ba a zata ba ya faru a kotu inda wasu shida daga cikin wadanda ake zargi suka yi gaggawar fita daga kotu kuma suka yanke jiki suka fadi , suna jan hankalin kafofin watsa labarai a wani yunkuri da aka shirya don jan hankali ga abin da ba daidai ba.”

“A kwanan nan rundunar ƴansanda ta ƙasa ta gurfanar da mutane 76 da ake zargi da aikata ta’addanci, cin amanar kasa da kone-kone. Wadannan Laifuka ne manya da su ka sa ake tsare da wadanda ake zargi.

“Tun lokacin da aka fara shari’ar nan, rundunar ƴansanda ta dage wajen bin ƙa’idojin Shari’a domin yi wa waɗanda ake zargin adalci,” in ji shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp