Kamfanin dakon wutar Lantarki na Nijeriya TCN ya tabbatar da sake lallacewar wutar kasar a ranara talata 5 ga watan Nuwamban 2024.
kamfanin yace wutar kasar ta sami tasgaro ne da misalin karfe 1:52pm, wannan na zuwa ne bayana da babbar tashar wutar lantarki ta Najeriya ta sake faduwa karo na 4 cikin mako guda.
Read Also:
mai magana da yawun kamfanin Ndidi Mbah ne ya bayyana hakan, wanda yace wannan ya biyo bayan wani tasgaro da layukan wutar suka samu.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa kafin faduwar wutar da misalin karfe 1:39 na yamma, kamfanin ya samar da wutar da ta kai megawatts 2,711, wadda kuma kafin lalacewar yana samar da megawatt 3,631.
Adadin wutar da aka samar dai a sanyin safiyar wannan rana da misalin karfe 6 ya kai Megawatt 3,934.77
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 44 minutes 29 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 25 minutes 54 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com