Home General Ma’aikatar Lafiya ta jihar Kano ta yabi Ƙananan Hukumomin Ajingi, Gaya, Wudil...

Ma’aikatar Lafiya ta jihar Kano ta yabi Ƙananan Hukumomin Ajingi, Gaya, Wudil kan Rigakafin Shan-Inna

Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ya nuna gamsuwa da yadda shirin rigakafin shan-inna yake tafiya a ƙananan hukumomin Ajingi, Gaya da Wudil.

Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da mai dauke da sa hannun jami’in yada labaran hukumar lafiya ta jihar Kano Ibrahim Abdullahi, wadda tace  Kwamishinan ya nuna gamsuwar ne a ranar Lahadin da ta gabata jim kaɗan bayan kammala duba aikin a wasu sassa na ƙananan hukumomin.

Ya ce ya ji daɗi sosai da yadda ya ga jama’a sun karɓi shirin hannu bibiyu, wanda shi ne jigon samun nasarar shirin a yankin, yana mai yaba wa ma’aikatan lafiya na ƙananan hukumomin wajen tabbatar da yi wa dukkanin yaran da suka cancanta rigakafin.

Kwamishinan ya jinjina wa shugabancin ƙananan hukumomin saboda kyakkyawan aikin da suka yi na bin tsare-tsare da aiki tare kamar yadda aka tsara tun daga matakin jiha, da kuma yadda suke halartar tarukan nazarin yadda aikin ya gudana a kowace rana.

Ya ce, “Abin farin ciki ne ganin yadda shugaban ƙaramar hukumar Gaya yake zuwa ko ina a yankin domin tabbatar da an yi wa yaran da suka cancanta rigakafin ba tare da tsallake yaro ko daya ba. Ƙari kan haka, shugaban ƙaramar hukumar yakan bayar da tallafin magunguna da kayayyakin aiki a asibitoci don inganta harkokin lafiya a yankin.

“Bugu da ƙari, an ga mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Wudil yana kai kawo a lungu da saƙo na yankin domin tabbatar da shirin ya cimma nasara a yankin.

Dakta Labaran, wanda Daraktan Daƙile Cututtuka Masu Yaduwa na Ma’aikatar Lafiya, Dakta Ibrahim Aliyu Gano ya wakilta, ya yaba wa jajircewar hakiman yankunan game da rawar da suke takawa don samun nasarar shirin a matsayinsu na iyayen ƙasa, da kuma yadda suke halartar tarukan duba yadda aikin ya gudana a kowace rana, inda a wasu lokutan suke tura wakilai idan ba za su samu damar zuwa ba.

Ya buƙaci iyaye da su ci gaba da kai yaransu da suka cancanta cibiyoyin yin rigakafi da aka ware ko kuma su bar ma’aikatan da ke bi gida-gida suna yi wa yaran rigakafin domin a daƙile ɓurɓushin cutar shan-inna da aka fara samu a wasu sassa na jihar nan, don haka akwai buƙatar haɗa hannu wajen tukarar matsalar.

Daga nan sai kwamishinan ya buƙaci jami’ai masu wayar da kan mutane kan kiwon lafiya a yankunan da su ƙara ƙaimi wajen ilimantar da al’umma su fahimci baƙatar da ake da ita ta su bai wa ma’aikata masu bi gida-gida cikakken haɗin kai domin kuɓutar da yaransu daga wannan cuta mai illa.

Dakta Labaran ya yaba da ƙoƙarin Gwamna Abba Kabir Yusuf na yadda ya mayar da fannin lafiya ɗaya daga cikin manyan ƙudurorin da gwamnatinsa ta bai wa fifiko wanda tuni kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu.

PRNigeria hausa

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp