Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ki bayar da belin Yahya Bello.
Tsohon gwamnan na jihar Kogi ya bayyana a gaban kotun yau Talata, domin neman beli kan shari’ar da ake yi masa.
Ana zargin Yahya da halasta kuɗin haram da suka haura naira biliyan 100 wanda ya karkata lokacin yana gwamna, a cewar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Da take yanke hukunci, mai shari’a Maryanne Anenih, ta ce an gurfanar da Bello ranar 27 ga watan Nuwamba, bayan da jami’ai suka kama shi ranar 26 ga watan. Sai dai an buƙaci belinsa ranar 22 ga watan na Nuwamba, kwanaki da dama kafin ma ya gurfana.
Mai shari’ar ta ce ya kamata a bukaci beli ne bayan an gurfanar da wanda ake ƙara.
“Buƙatar beli da Yahya ya yi tun da farko ba ya kan tsari, don haka ne muka yi watsi da shi,” in ji mai shari’a Maryanne Anenih.












