Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo a birnin Abeokuta na jihar Ogun.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar NNPP tare da tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke, sun gana da Obasanjo a gidansa da ke birnin Abeokuta.
Cikin wani saƙo da tsohon gwamnan na jihar Kano, ya wallafa a shafinsa na X, ya ce a lokacin ganawar sun tattauna abubuwan da suka shafi ƙasa, ciki har da makomar siyasar ƙasar.
“Mun yaba da yadda Baba ya nuna mana karimci da cikakken goyon baya,” kamar yadda ya wallafa.











