Shugabannin ƙungiyar ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas za su gana yau Lahadi a Abuja, domin tattauna batutuwan da suka shafi haɗin kai da tsaro da kuma tattalin arzikin yankin.
Ana sa ran batun ficewar ƙasashen yankin Sahel daga ƙungiyar ne zai zama babban ajandar taron na yau.
Ƙa’idar da Ecowas ta gindaya ta sanarwar shekara guda kafin ficewar ƙasa daga ƙungiyar – wanda ƙasashen Mali da Burkina Faso da Nijar suka yi – zai cika a watan Janairu mai zuwa.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
A makon da ya gabata ne, shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya shaida wa shugaban Jamus da ya ziyarci ƙasar, Frank-Walter Steinmeier, cewa muradun walwalar ‘yan ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar ne babban abin da ke ran shugabannin Ecowas.
Inda ya alƙawarta yi amfani da diplomasiyya da hikima wajen maido da ƙasashen cikin ƙungiyar.
Shugaba Tinubu – wanda shi ne shugaban Ecowas – ya sha amfani da hanyoyin diflomasiyya don ganin ya janyo hankalin ƙasashen na yankin Sahel domin su koma cikin ƙungiyar.











