Gwamnatin Najeriya tare da haɗin gwiwar bankin duniya sun kasafta dala miliyan 600 domin faɗaɗa hanyoyin karkara a ƙarƙashin zagaye na biyu na shirin inganta hanyoyin kasuwanci da noma wato Rural Access and Agricultural Marketing Project (RAAMP).
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Minista a ma’aikatar noma da samar da abinci, Sabi Aliyu Abdullahi ne ya bayyana a wani taron manema labarai da ya yi a Abuja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ya ce tsarin kashe kuɗin zai kunshi dala miliyan 500 da bankin duniya zai bayar, sai kuma gwamnatin tarayya da gwamnonin Najeriya da za su haɗa dala miliyan 100.
Ya ce inganta hanyoyin zai taimaka wajen sauƙaƙa kai amfanin goma kasuwanni da inganta tattalin arziki.











