Home General Fannin tsaro ya samu kaso mafi yawa a kasafin 2025 da shugaba...

Fannin tsaro ya samu kaso mafi yawa a kasafin 2025 da shugaba Tinubu ya gabatar

Fannin tsaro da manyan ayyuka da lafiya da ilmi sun samu kaso mai yawa cikin kasafin kuɗin shekarar 2025 da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gabatarwa da haɗakar zauren majalisun dokokin Najeriya wanda ya kai naira tiriliyan 47.9

A jawabin da ya yi a zauren majalisar dokokin domin amincewa da shi, Tinubu ya ce an warewa bangaran tsaro naira tiriliyan 4.91.

Manyan ayyukan da za a yi a shekara mai zuwa kuwa an ware naira tiriliyan 4.06 sai fannin kiwon lafiya da aka warewa naira tiriliyan 2.4 sai kuma fannin ilmi da aka warewa tiriliyan 3.5.

Tinubu ya ce kasafin zai taimaka wurin rage tsadar rayuwa daga kashi 34.6 zuwa kashi 15 a shekarar 2025, kuma zai sanya farashin dalar Amurka ya sauka daga 1700 zuwa 1500.

A kasafin na 2025 shugaban ya ce ana sa ran haƙo ganga ɗanyan mai miliyan 2.06 a kowacce rana, za kuma a samu raguwar shigo da tataccen man fetur cikin Najeriya tare da samun ƙaruwar fitar da tatacccen man.

A yayin gabatar da kasafin kuɗin Tinubu ya godewa ƴan Najeriya bisa hadin kan da yake samu a sauye-sauyen da gwamnatinsa ke yi cikin watanni 18 da suka gabata.

Ya ƙara da cewa tattalin arziƙin ƙasar na murmurewa kuma gwamnatinsa za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace don ci gaban tattalin arziƙi, kuma gwamnati ba za ta ja da baya ba kan matakan da take ɗauka.

A bangaran samar da abinci shugaban ya ce ba za su yi wasa wurin tabbatar da wadatar da ƙasar da abinci, kuma suna ɗaukar matakan tabbatar da cewa ƴan Najeriya ba sa kwana da yunwa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp