Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce matakan da suka ɗauka na inganta tattalin arzikin ƙasar sun fara haifar da ɗa mai ido.
Tinubu ya bayyana haka ne a cikin jawabin da ya gabatar a majalisar dokoki, inda ya ce, “gyare-gyaren da muka yi sun fara haifar da ɗa mai ido.
“Ƴan Najeriya sun kusa fara cin gajiyar ingantaccen tattalin arziki, Ƙasarmu tana samun ci gaba sosai a fagen tattalin arziki.”
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ya ƙara da cewa tattalin arzikin Najeriya ya inganta, inda a cewarsa ya haɓaka da kashi 3.46 a rubu’i na uku na shekarar 2024, daga kashi 2.54 a rubu’i na uku na shekarar 2023.
Sai dai shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya yi kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya ja kunnen “ministocinsa masu taurin kai” waɗanda ba sa amsa gayyatar majalisar dokoki.
Akpabio ya ce bai kamata irin waɗannan ministocin su samu gurbi a gwamnatinsa ba.
Akpabio ya bayyana haka ne a ranar Laraba, a lokacin da shugaban ƙasar yake gabatar da kasafin kuɗin 2025.
“Waɗanda suke ƙin amsa gayyatar majalisar dokoki ba ƴansiyasa ba ne, don haka bai kamata su samu gurbi a gwamnatinka ba,” kamar yadda Akpabio ya bayyana wa Tinubu.











