Home General Mutune dari ne suka mutu a Najeriya dalilin gobara a shekarar 2024

Mutune dari ne suka mutu a Najeriya dalilin gobara a shekarar 2024

Hukumar Kashe Gobara ta Ƙasa ta bayyana cewa, Najeriya ta yi asarar rayuka mutane 100 da dukiyar da ta kai Naira biliyan 67.1 sakamakon ɓarkewar gobara a shekarar 2024.

Hukumar ta kuma ce an ceto rayuka al’umma 30,890 da kadarorin da darajarsu ta kai N1.94tr daga ɓarnar da aka samu a lokacin ɓarkewar gobara daban-daban a faɗin ƙasar nan a shekarar 2024.

Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Ƙasa, Abdulganiyu Jaji ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Abuja ranar Juma’a.

Ya ce, “A shekarar 2024, hukumar kashe gobara ta yi nasarar ceto dukiyoyin da darajarsu ta kai Naira tiriliyan 1.94 tare da yin asarar dukiyoyi da aka yi ƙiyasin ta kai ta Naira biliyan 67.1.

“A cikin wannan shekarar, Hukumar kashe gobara ta kai ɗauki kashe gobara da sauran abubuwan gaggawa inda aka ceto rayuka 30,890 yayin da mutane 23 suka rasa rayukansu. A matsayinmu na ’yan Najeriya, muna cikin waɗanda ke jajantawa iyalan waɗanda suka rasu da kuma ‘yan uwansu.”

Ya danganta yawancin abubuwan da suka faru da sakaci da rashin bin ƙa’idojin kariya.

Jaji ya buƙaci ‘yan Najeriya da su ƙara taka tsantsan a lokacin bazara, inda ya ƙara da cewa haɗarin gobara yana da yawa a wannan kakar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp