Gwamnatin Najeriya ta amince da kamfanonin jiragen sama guda huɗu domin jigilar maniyyata Hajjin bana.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban hukumar jin daɗin alhazai ta Najeriya, NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman ya fitar a ranar Lahadi, inda ya ce an zaɓi kamfanoni huɗu ne daga cikin guda 11 da suka nuna sha’awar aikin jigilar maniyyatan, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.
Ya ce kamfanonin huɗu su ne: Air Peace Ltd, da wani kamfanin ƙasar Saudiya mai suna Fly-Nas da Max Air da kuma UMZA Aviation Services Ltd.
Ya ƙara da cewa kwamiti mai mutum 32 da aka kafa a ranar 26 ga Nuwamban bara ne suka zauna suka tantance kamfanonin, kafin suka amince da guda huɗun











