Home General NLC ta sanya wa kamfanonin Layin waya sharudda a Nijeriya

NLC ta sanya wa kamfanonin Layin waya sharudda a Nijeriya

Kungiyar ƙwadago ta Najeriya, NLC ta nemi kamfanonin sadarwar da ke aiki a kasar su janye sabon farashin su kuma koma wa tsohon farashi cikin gaggawa.

A wata takardar bayan taro da ƙungiyar ta fitar wanda ta gudanar ranar Talatar nan a birnin Lokoja na jihar Kogi, NLC ta ɗauki wasu matakai guda bakwai kan al’amarin kamar haka:

  • Janye ƙarin farashin da komawa tsohon farashi har zuwa lokacin da kwamitin da ƙungiyar ta kafa ya kammala gudanar da bincike.
  • Ƙungiyar ta buƙaci ma’aikatan Najeriya da sauran ƴan ƙasa da su ƙaurace wa kiran waya ko amfani da datar kamfanonin MTN da Airtel da Glo a kowacce rana daga ƙarfe 11:00 na safe zuwa ƙarfe 2:00 na rana na kowace rana har zuwa ƙarshen watan Fabrairu.
  • Ta umarci ƴan Najeriya da su daina sayen data daga kamfanonin
  • Ƙungiyar na buƙatar kamfanonin su dawo wa Najeriya da kuɗaɗen da suka kwashewa ƴan ƙasar
  • Ƙungiyar za ta jagoranci rufe ayyukan kamfanonin ranar 1 ga watan Maris idan dai har ba su janye sabon ƙarin da suka yi ba ya zuwa ƙarshen watan Fabrairu.
  • Ƙungiyar ta umarci dukkannin rassanta na jihohi da su zaburar da mambobinsu gabanin 1 ga watan na Maris.
  • Ƙungiyar ta umarci dukkan sauran sassanta da su ja hankalin mambobinsu wajen ƙaurace wa kira ko amfani da datar kamfanoni a sa’o’in da aka ayyana
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp