Home General Ƙudirin haraji ya tsallake karatu na biyu a Majalisar Wakilan Najeriya

Ƙudirin haraji ya tsallake karatu na biyu a Majalisar Wakilan Najeriya

Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da ƙudirin haraji a karatu na biyu, bayan zazzafar muhawara kan ƙudirin tsakanin ‘yan majalisar.

Tun da farko majalisar ta haɗe duka ƙudurorin harajin huɗu da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya aike mata a shekarar da ta gabata zuwa ƙuduri guda kafin fara muhawara a kansa.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Farfesa Julius Ihonvbere ne ya jagoranci muhawarar, wanda ya ce kuɗurin zai taimaka wajen farfaɗo da fannin karɓar haraji na ƙasar.

Farfesa Ihonvbere ya yaba wa ƙoƙarin ƙungiyar gwamnonin bisa kwaskwarimar da suka yi wa ƙudurin, da nufin ,magance matsalolin da aka yi fargabarsu tun da farko.

Ƙudirin harajin ya haifar da zazzafar muhawara takanin ‘yan ƙasar, musamman waɗanda suka fito daga yankin arewacin ƙasar, inda suka riƙa zargin cewa sabon ƙudirin zai cutar da yankin.

A farkon wannan shekarar ne ƙungiyar gwamnonin ƙasar suka amince da kuɗurin bayan sun yi masa kwaskwarima dangane da yadda za a raba harajin VAT.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp