Home Bincike Bincike: Shin da gaske ne Matar Gwamnan Jihar Katsina, Fatima Radda, ta...

Bincike: Shin da gaske ne Matar Gwamnan Jihar Katsina, Fatima Radda, ta “Lika” Dalar Amurka a wurin biki?

Wani faifan bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta na zamani, musamman Instagram, da aka hada da wani rubutu dake cewa an gano  Matar Gwamnan Jihar Katsina (first Lady) Fatima Dikko Radda, tana watsa (lika) a wurin biki.

Faifan bidiyon dake da tsahon dakika (second) 9 tare da rubutun dake kalubalatar matar Gwamnan, kan yadda take wadaka da dukiyar mutanen da ke fama da matsalar ta’adanci, garkuwa da mutane, tarin mabarata, gami da tarin yaran da basa zuwa makaranta.

Rubutun ya zarge ta tana yin liki da dalar Amurka a wajen bikin wanda a karshe aka sanya alamun kuka dakenuna yadda mai rubutun yake bakin ciki da abin da ta aikata.

Rubutun cewa yayi:

“Matar Gwamnan Katsina Kenan dake watsa Dalar Amurka da suka sata a wajen biki………????

“A dai wannan jihar ta katsina dake da Matsalar Ta’addanci, garkuwa da mutane ta yi kaka gida, jihar da ke ta darin yara kanana da basa zuwa makaranta, wadanda ke fama da yunwa, da matsanancin talauci da bakin ciki????

“Wannan wane irin rashin mutunci, da albazaranci da take aikatawa..????”

Tantancewa:

A kokarin PRNigeria na tantance ikirarin, ta yi nazari da bincike na tsanaki gami da hada bidiyon dake nuna matar gwamnan da wani faifen bidiyon dake nuna yadda take bayar da tallafin naira miliyan 2 domin rage bashi ga masu fama da cutar cancer a jihar.

Bincike kuma ya nuna cewa dukkannin bidiyon guda biyun da sun nuna yadda

Suka yi kamanceceniya, sai da kuma an dauke su ne a mabambanta wurare.

Bugu da kari PRNigeria ta nazarci sautin dake tashi a kasn bidiyon (background music of the video) tambayar anan itace, mene ya kawo ikirarin da aka yin a zagin matar Gwamnan na lika dalar Amurka, amma sautin dake kasa na wani mawakin jausa ne dake koda ta yana cewa “ Fatima Radda, Matar Gwamnan inuwa bakya kyamar kowa, haka kuma tana son kowa. Da ganin ta kaga ta gari…”

Wani bincike kwakkwafi kan faifen Bidiyon da aka gudanar ta hanyar rarrabashi daki-daki ta hanyar amfani da Manhajar Yandex. Ya tabbatar da cewa matar gwamnan ta lika dalar Amurka a yayin bikin ‘yar uwa ko dan uwanta da aka gudanar ranar Asabar 25 ga watan Janarun 2025 a jihar Katsina.

Wani bincike na kashin kai da aka yi amfani da wasu kalmomi dake da alaka da labarin, ta tabbatar da cewa Matar Gwamnan ta aikata, a takaice talika dalar Amurka a yayin bidirin bikin.

A Takaice:

Hujjojin da PRNigeria ta tattara ta hannun tawagarta dake gudanar da binciken sahihancin labara, sun tabbatar da cewa Matar Gwamnan jihar Katsina Hajiya Fatima Dikko Radda ce take yin liki a wajen bikin Dan uwanta da aka gudanar ranar Asabar, 25 ga watan Janairu 2025, a jihar Katsina

Hukunci:

Saboda haka PRNigeria ta yanke hukunci kan ikirarin da aka yi kan matar Gwamnan jihar ta Katsina dake cewa an ganta a wani faifen bidiyo tana liki kudin Amurka, wannan ikirarin gaskiya ne.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp