Sojojin Najeriya karkashin dakarun Operation WHIRL STROKE (OPWS) sun sanar da kashe ƴanbindiga uku, sannan suka lalata mazauninsu tare da ƙwace makamai a ƙaramar hukumar Karim Lamido da ke jihar Taraba.
Sojojin sun samu nasarar ce a ranar 5 ga Afrilu, kamar yadda kakakin sashen Olubodunde Oni ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Sanarwar ta ƙara da cewa da sojojin suka isa yankin Chibi, sai ƴanbindigar suka fara tserewa, “inda sojojin suka bi sahunsu suka yi musayar wuta, inda dakarunmu suka kashe ƴanbindigar guda uku, sannan suka tarwatsa mazauninsu, tare da ƙwato makamai.”
Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin na Najeriya sun yi sintiri a yankin Dutsen Zaki da Achalle a kwanakin baya, inda suka tarwatsa mazaunan ƴanbindiga da dama.












