Home WASANNI Chelsea da Newcastle na Harin Coulibaly, Liverpool na Neman Siyan Marcos Sensi

Chelsea da Newcastle na Harin Coulibaly, Liverpool na Neman Siyan Marcos Sensi

Karim Coulibaly

Chelsea da Newcastle na Harin Coulibaly, Liverpool na Neman Siyan Marcos Sensi

 

Liverpool ce kan gaba a neman siyen ɗan wasan Bournemouth da Argentina, Marcos Sensi, da kwantaraginsa zai ƙare a wannan kaka. (i paper)

Manchester City na dab da kamala tayin siyen ɗan wasan Feyenoord Givairo Read, sai dai Bayern Munich ita ma na harin ɗan wasan. (Sky Sports)

Livepool na son ɗauko ɗan wasan Newcastle Anthony Gordon, da ɗan wasan Everton Iliman Ndiaye, a yunƙurinsu na ƙara inganta ƴan wasan gaban ƙungiyar a kaka mai zuwa. (Teamtalk)

Tsohon ɗmai horar da Chelsea da Manchester United, Jose Mourinho na kan gaba cikin wanda Newcastle ke son ya maye gurbin Eddie Howe, idan har suka yanke shawarar sallamar mai horar da ƴan wasan ƙungiyar. (Talksport)

Bournemouth na mataki na gaba wajen ɗaukar tsohon mai horar da ƴan wasan Borussia Dortmund da RB Leipzig Marco Rose, kasancewar ba ya tare da wata ƙungiyar a halin yanzu. (Telegraph – subscription required)

Chelsea da Newcastle na cikin ƙungiyoyin da ke harin dan wasan baya na Jamus Karim Coulibaly, bayan ƙwazon da ya yi a kakkar wasanni a Werder Bremen. (Bild – in German)

Juventus ta sa ido kan mai tsaron ragar Liverpool Alisson, yayin da Manchester City ke harin ɗan wasan tsakiya Bernardo Silver, a yunkurin sun na ƙara inganta tawagar yan wasan su a kakar wasanni. (Corriere dello Sport – in Italian)

Newcastle United na shirye-shiryen ganin sun sake gwada taya siyen Ousmane Diomande a kakar wasanni mai zuwa. Newcastle dai ta fara nuna sha’awar ɗaukar ɗan wasan ne tun a watan Janeiru, sai dai Sporting ta ƙi amincewa da tayin na Euro miliyan 40. (Football Insider)

Ɗan wasan bayan Como Jacobo Romon, na ci gaba da ɗaukar hankalin ƙungiyoyin da ke Ingila ciki har da Arsenal da Chelsea. (Teamtalk)

Arsenal na shirye-shiryen siyar da Gabriel Jesus, da Kai Havertz a kaka mai zuwa, domin samun kuɗin da za su siyo ɗan wasan Atlantico Madrid Julain Alvarez. (Caughtoffside)

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp