Ƙasashen Amurka da Saudiyya sun fitar da sanarwar haɗin gwiwa, ta maraba da tattaunawar farko ta kai tsaye tsakanin ɓangarorin da ke yaƙi da juna makwanni uku da suka wuce a Sudan.
Nan gaba a yau ake sa ran za su halarci wani zama na sulhu abirnin Jedda na ƙasar Saudiyya.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Abin da zai kai ɓangarorin biyu Jedda shi ne batutuwa biyu, tsagaita wuta da kai agaji ga ‘yan Sudan, sai dai ɓangaren RSF ba su ba da tabbacin halarta ba.
Masu shiga tsakanin sun buƙaci sojojin gwamnatin Janaral Abdul Fatta al-Burhan da jagoran dakarun RSF Muhammad Hamdan Dagalo sun amince da tsagaita wuta ta dindindin, bayan wadda ta fara aiki shekaran jiya ta rushe a jiya juma’a.











