Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya ce kwanakin ɗan bindiga, Bello Turji da sauran manyan ƴanbindiga da suka addabi ƙasar sun kusa ƙarewa a daidai lokacin da sojoji suke cigaba da aiki a jihar Zamfara da sauran jihohin Arewa maso Yamma.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ya ce kashe Kachalla Halilu Sububu, wanda ƙasurgumin ɗanbindiga ne ya cikin nasarorin da sojojin suke samu.
Janar Christopher ya ƙara da cewa wani aikin soji na musamman mai suna “Fansar Yamma a Arewa maso Yamma,” da za a ƙaddamar ne zai kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin.
Ya ce za a ƙara tura wasu jiragen yaƙi zuwa jihar domin cigaba da aikin sojin, kamar yadda babban hafsan ya bayyana a ziyararsa ga Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal.











