Dakarun sojin Nijeirya karkashin rundunar Operation hadin kai ta sami nasarar hallaka kwamandan mayakan kungiyar ISWAP, Ibn Kaseer tare da wasu mayakan kungiyar guda uku a wani hari da suka kai dajin Sambisa a safiyar ranar Alhamis.
Zagazola makama ya bayyana cewa wani rahoton sirri ya tabbatar da yadda dakarun sojojin karkashin rundunar sojoji ta 21, sun sami nasarar a yayin wata kora da suka kai a kauyen Kashomeri.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Kwamandan mayakan na ISWAP ta ya addabi al’ummar Geizuwa da Yale ya yi yunkurin samun mafaka a yankin na Kashomeri shi da iyalansa.
Majiyar dai ta tabbatar da cewa bayan bankado maboyar ta sa ne dakarun suka hallaka shi tare da wasu mayakansa guda biyu da aka bayyana a matsayin Bulamadu, sai dai majiyar tace lamarin ya faru ne bayan da mutanen sa suka fita wani aikin taaddanci a yankin Jalumeri.
Haka kuma bayan hallaka kwamandan rundunar ta sami nasarar kubutar da mata hudu da yara kanana, yayin da wasu daga cikin ‘iyalan mayakan na ISWAP suka mika wuya ga dakarun sojojin a Kunduga.











