Jogaran adawar Najeriya, Atiku Abubakar ya soki gwamnatin ƙasar, kan abin da ya kira gurfanar da ƙananna yara a gaban kotu domin yi musu shari’a.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa X, tsohon mataimakin shugaban ƙasar, ya ce ya damu da bidiyon yaran da aka nuna ”bayan yunwa ta yi musu illa, a inda aka tsare su”.
”Wannan abu na tayar da hankali ya tunamin da zaluncin ‘yan aƙidar Nazi, tare da ƙara fito da yadda gwamnati ke wasarere da rayukan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, musamman ƙananan yara”, in ji Atiku Abubakar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa ƙananan yara cikakken ‘yancin mutuntawa, amma abin mamakin sai suka rasa hakan a Najeriya, a cewar Atikun.
”Ina mamakin mutumin da ke iƙirarin kare dimokraɗiyya, har ya jagoranci zanga-zanga a baya, amma a yanzu yake barazana ga waɗanda ke yunƙurin nuna damuwarsu kan halin da suka shiga sakamakon manufofinsa masu tsauri”, in tsohon ɗan takarar shugabancin ƙasar.
Ya ƙara da cewa ƙananan yaran -waɗanda su ne suka fi cutuwa kan manufofin gwamnatin Tinubun na da damar gudanar da zanga-zangar lumana kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba su dama.











