Kuɗin da aka kashe domin shigo da man fetur daga ƙasar Malta ya ƙaru zuwa N766.81 a rubu’i na uku na shekarar 2024, kamar yadd alƙaluma hada-hadar ƙasashen waje da hukumar ƙididdiga ta ƙasa NBS suka nuna.
Duk da cewa rahoton bai tantance waɗanne irin kayayyaki ne aka shigo da su daga Malta ba, amma lamarin ya ja hankalin mutane saboda zargin da Aliko Dangote ya yi a baya cewa ana shigo da man fetur daga ƙasar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Sai dai bincike y nuna cewa babu bayanin shigo da wani kaya daga Malta a rubu’i na farko da na biyu na shekarar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana.
Amma a rubu’i na uku, sai aka samu ƙaruwar shiga da kayayyakin daga ƙasar.
Ƙididdigar ta NBS ta nuna cewa Malta ce ƙasa ta biyar a cikin ƙasashen da aka fi shigo da kayayyakinsu Najeriya












