Home General An buƙaci NNPCL ya yi bayani kan ‘ɓatan’ ɗaruruwan biliyoyi

An buƙaci NNPCL ya yi bayani kan ‘ɓatan’ ɗaruruwan biliyoyi

Kungiyar SERAP, mai fafutukar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta yi kira ga shugaban kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL Mele Kyari, ya yi bayani game da zargin bacewar sama da Naira biliyan 825 na kudin shigar mai da kuma dala biyan biyu da miliyan ɗari biyar da aka ware domin gyaran matatun man kasar da kuma kudaden shigar mai.

Bukatar ta biyo bayan rahoton shekara ta 2021 da babban mai binciken kudi na tarayya ya gabatar, wanda ya nuna matukar damuwa game da yadda ake tafiyar da kudaden gwamnati a hukumar ta NNPC.

Wani binciken da SERAP ta yi kwanan nan, wanda aka buga a ranar 27 ga Nuwamba, 2024, ya nuna yadda alkaluman wasu kudade suka ci karo da juna, ciki har da wasu da suka bace ko ba a iya tantance abun da aka yi da su ba.

Wannan ya hada da Naira biliyan 825 da ake zargin an cire na kudin danyen man da aka sayar, da kuma dala biliyan biyu da miliyan dari biyar na gyaran matatun man kasar tsakanin shekarar 2020 zuwa 2021.

Ofishin babban mai binciken kudi ya nuna cewa watakila an karkatar da wadannan kudade kuma ya bukaci a gudanar da cikakken bincike tare da kuma kwato su.

A cewar Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, dole ne a mika wadanda ke da hannu wajen karkatar da kudaden ga hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC da sauran laifuka masu zaman kansu domin gudanar da bincike tare da gurfanar da su gaban kuliya.

A ranar Asabar din da ta gabata ne dai tsohon shugaban Najeriyar Olusegun Obasanjo ya yi kira da a gurfanar da shugabannin NNPCL a gaban kotu, bisa zarginsu da yin almundahana da cin hanci da rashawa, a wani kakkausan suka kan yadda Najeriya ke tafiyar da matatun man fetur guda hudu mallakin gwamnati.

Obasanjo ya bayyana takaicinsa kan yadda matatun man ke ci gaba da gazawa da kuma yadda ake karkatar da kudade.

Ya ba da misali da makudan kudi dala biliyan 1.5 da aka kashe a matatun man ba tare da samun wani gagarumin ci gaba ba. “Har yanzu matatun nan na cikin mawuyacin hali wanda har yanzu ba su da wani amfani,” in ji shi. “Ba za ku iya sayar da su ko da dala miliyan 200 ba.”

Da yake sukar irin rawar da NNPC ke takawa a lamarin, Obasanjo ya bayyana cewa shugabannin kamfanin ya kamata a ɗorawa alhaki”

“NNPCL sun san cewa matatun man nan ba za su yi aiki ba, amma saboda sun san za su zame musu wata hanya ta sata sai suka ci gaba da zuba kudi a kansu, idan da a al’ummar da suka san mutuncin kansu ne da yanzu shugabannin kamfanin na kurkuku” in ji shi.

Sai dai kamfanin man na NNPCL ya musanta dukkan waɗannan zarge zarge har ma ya gayyaci tsohon shugaban kasar domin gudanar da rangadin duba yadda matatun man ƙasar suke.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp