Home General Harin sojin saman Najeriya ya sake hallaka tarin fararen hula a Zamfara

Harin sojin saman Najeriya ya sake hallaka tarin fararen hula a Zamfara

Nigeria Airforce

Sojin saman Najeriya sun sake hallaka fararen hula aƙalla 16 yayin wasu hare-hare da suka nufaci kaiwa kan ƴan bindigar da ke ƙauyuka a ƙananan hukumomin Zurmi da Maradun na jihar Zamfara, fararen hular da bayanai ke cewa galibinsu ƴan sakai ne da suka gwabza faɗa da ƴan bindigar.

Rahotanni sun bayyana cewa tun farko ƴan sa kan da ke taimakawa wajen fatattakar ƴan bindiga a ƙauyukan ne suka nemi ɗauki don taimakawa musu wajen kammala murƙushe ƴan bindigar da suke tsaka da faɗa da su, amma kuma Sojojin saman na Najeriya suka yi tsammanin su ne ƴan bindigar inda nan ta ke suka buɗe musu wuta.

Tuni dai gwamnan jihar ta Zamfara Dauda Lawal ya aike da saƙon jaje ga iyalai da ƴan uwan ƴan sa kan da suka mutu a wannan hari yayinda ya jinjinawa Sojin na Najeriya game da namijin ƙoƙarin da suke wajen kakkaɓe barazanar ƴan bindiga a jihar.

Wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ta miƙa sakon ta’aziyya kan kisan ƴan sa kan waɗanda ta ce sun nuna matuƙar jajircewa a wanzar da zaman lafiya ga al’ummar ta Tungar Kara a ƙaramar hukumar Zurmi wajen kange barazanar ƴan bindigar da ke afkawa jama’a.

Rahotanni sun ce ƴan sa kan, na kan hanyarsu ta barin Gidan Makera ne na yankin Boko duk dai a ƙaramar hukumar ta Zurmi lokacin da haɗarin ya faru a yau Lahadi, da ya kai ga rasa rayukan 16 daga cikinsu.

Wannan tsautsauyi na zuwa a dai dai lokacin da wasu ƴan sa kan fiye da 30 suka rasa ransu cikin makon jiya can a jihar Katsina bayan da wani gungun ƴan bindiga ya afka musu, lamarin da ke nuna gagarumar asarar da aka fuskanta a ƙoƙarin da fararen hula ke yi na bai wa kansu kariya daga barazanar ƴan bindiga.

A cewar wasu bayanai tsautsayin ya faru ne a lokacin da Sojin saman na Najeriya ke kan hanyarsu ta dawowa daga luguden wutar da suka yi wa maɓoyar ƴan bindigar a garin na Tungar Kara yau lahadi, kwatsam kuma sai suka ci karo da ayarin ƴan sa kan dalilin ya sanya suka tsammaci cewa ƴan sa kan, wani ɓangare ne na ƴan bindigar suke ƙoƙarin guduwa.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Sojin Najeriya ke kashe tarin fararen hula ko kuma ƴan sa kai ko ma ƴan gudun hijira bisa tsammanin kasancewarsu ƴan bindiga ko ƴan ta’adda ba.

Masana dai na alaƙanta kuskuren kisan ƴan sa kan, da yadda ake gaza musayar bayanai tsakanin irin waɗannan mutane da ke taimakawa zaman lafiyar yankuna da kuma jami’an tsaro.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HURIWA ta Soki Ƴan Sanda da NDPC Kan Jinkirin Binciken Zargin Kutse da aka yi wa Bayanan NIPSS da ya Shafi Jami’in Sojan RuwaƳa'yan El-Rufai Sun Shiga Rikici Yayin da Bashir ya Zargi Bello da Shan Muggan Kwayoyi da Cin Amanar suTsaro, Fafutuka da Nauyin Tabbatarwa Daga Mukhtar Ya’u MadobiONSA ta Fitar da Faɗakarwar Tsaro, ta Bukaci Ƴan Najeriya su ƙara Yawan Tsawaita TsaroHukumar DSS ta Dakatar da Shari'ar Sowore Kan Laifukan Intanet Har Sai Bayan Zaben Shugaban Kasa na 2027Gwarzo ya ba da Gudummuwar ₦10m ga Horarwa na Musamman na PRNigeria Bayan ya ba da Gidansa na Abuja Don Cibiyar Koyon Aikin Jarida2027: Bayan Takardu da Sauran Tsoffin Maganganu Marasa Amfani, ‘Yan Najeriya Sun Cancanci Kamfen Din da Ya Dace Da Matsaloli  Daga Kabir AkintayoGwamnati Tarayya ta Bayyana Bas 100 Masu Amfani da Wutar Lantarki Don Rage Wa Ma’aikatan Gwamnati Matsalar SufuriƳan Ta’adda na Amfani da Kafafen Sada Zumunta da Dandamalin Aikin Tura Kuɗi Don Tallafa Wa Ayyukansu — BukartiBinciken Gaskiya na PRNigeria: Ta Karyata Da’awar Tony Elumelu ta Cewa An yi Satar Man Fetur Kashi 97% Kafin Zamanin TinubuMeyasa Mutuwar Bazata Take Daukar Masu Alheri ta Bar Mugaye ? Na Yushau A. ShuaibSojoji Sun Kama Bindigar AK-103 Da Aka Boye a Cikin Jakar Gero, Sun Kama Mutum Uku A ZamfaraSojoji Sun Kama Shahararren Shugaban Ƴan Bindiga, 'Sanusi Maigilas' a Dajin Katsina2027: Yadda Zan Magance Rashin Tsaro, In Magance Matsalolin Tattalin Arziki da Zamantakewa a Kwara — Zakari MohammedLabarin NIPSS Mai Damuwa: Lokacin da Jami'in Sojan Ruwa Ya Cin Zarafin Mawallafi Daga Nuhu Mohammed
X whatsapp