Home General An sace kayan wutar lantarki a birnin Abuja

An sace kayan wutar lantarki a birnin Abuja

Hukumar rarraba lantarki ta Najeriya (TCN) ta sanar da cewa wasu mutane sun ɓarnata tare da sace kayan wuta da ke samar da lantarki ga wasu sassa na Abuja, babban birnin ƙasar.

Sanarwar da hukumar ta fitar a jiya Juma’a ta ce “an lalata layin wutar lantarkinta na 132kV da wayoyin ƙarƙashin ƙasa waɗanda ke kai lantarki zuwa cikin ƙwaryar Abuja da unguwannin da ke kewaye, lamarin da ya kawo katsewar lantarki”.

Lamarin dai ya jefa unguwannin Abuja da dama cikin duhu, tare da haifar da wahalahalu ga al’umma.

Sanarwar, wadda ta samu sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Ndidi Mbah, ta ce wayoyin su ne ke kai lantarki ga cibiyoyin rarraba lantarki na kamfanin AEDC domin samar da lantarki ga al’umma.

“Lamarin wanda ya faru a kusa da Millenium Park da ke Abuja, ya shafi fiye da kashi 60 cikin ɗari na lantarkin da ake samar wa birnin,” in ji sanarwar.

Bayanin ya tabbatar da cewa maɓarnatan sun sace wayoyin lantarki da sauran kayan wuta da dama.

Unguwannin da abin ya shafa sun haɗa da Maitama, da Wuse, da Jabi, da Life Camp, da Asokoro, da Utako da kuma Mabushi.

Hukumar ta TCN ta ce ta tura jami’anta domin yin gyara a inda aka sace kayan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Tarayya ta Kaddamar da Kwamitin Bincike Kan Mutuwar Ma'aikatan Haƙar Ma'adinai 37 a Hukumar Kula da Haƙar Ma'adinai ta NSCDCMajalisar Dattawa ta 10 da Ma'anar Jagorancin Majalisa Daga Kabir AkintayoDarakta Janar na NITDA ya yi Kira da a Hada Hannu Kan Tsarin AI a Taron Manyan ShugabanniƳancin Sanin Gaskiya: Bayani Game da Tsarin Gudanar da Harkokin Sadarwa na Najeriya Daga Franklyn Ginger-EkeHOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna Yusuf
X whatsapp