Home General Bincike: Shin da gaske ne CP Hauwa Ibrahim ita ce mace ta...

Bincike: Shin da gaske ne CP Hauwa Ibrahim ita ce mace ta farko da ta fara zama kwamishinan ‘yan sanda daga Arewacin Nijeriya?

Wani labari dake yawa a kafafen sada zumunta na zamani, musamman shafin X da aka fi sani da twitter, da kuma shafin Instagram dake cewa sabuwar kwamishinan ‘yan sanda (CP), Hauwa Ibrahim, ita ce mace ta farko da ta fara kaiwa zuwa wannan mukamin daga yankin arewacin Nijeriya. Kamar yadda wata jarida daga jihar Kano ta wallafa, “itace mace ta farko daga Arewacin Nijeriya da ta zama kwamishinan ‘yan sanda.”

PRNigeria ta gudanar da binciken sahihancin labara da wasu kalmomi dake da alaka da wannan labara tare da yin bincike kwakkwafi na kai da kai domin tabbatar da gaskiyar labarin. Binciken kuma ya nuna cewa akwai mata da dama daga yankin na Arewacin Nijeriyar da suka kai wannan matakin na kwamishinan ‘yan sanda (CP) har wasu ma sun wuce mukamin

  1. AIG Farida Waziri:

Farida Waziri, guda ce cikin fitattun mata, wadda ta shiga rundunar ‘yan sandan Nijeriya 1965/1966. Wanda ta kai har zuwa  mataimakiyar babban sifetan ‘yan sandan na kasa (AIG) sannan kuma ta yi aiki matsayin kwamishinan ‘yan sanda a sashen lura da laifukan damfara. Wadda ta smai gagarumar nasarar da ba’a taba samu a kasar ba kafin ta. Daga bisani ta zama shugabar hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC inda ta bayyana gogewarta a fannin tabbatar da doka da oda.

  1. AIG Aisha Abubakar Baju:

Tana matsayin guda cikin fitattun mata daga yankin arewacin Nijeriya da suka kai har matakin Mataimakin babban sifeton ‘yan sandan kasar wadda ta fito daga jihar Taraba, an fi sanin ta da Sarauniyar Mambila. An haifeta a shekarar 1971 a jihar Adamawa, in da tayi Digirin ta na farko a Jami’ar AHmadu Bello, dake Zariya, a shekarar 1994, wadda ta karancin fannin maganin Dabbobi (DVN). Ta shiga rundunar ‘yan sanda a matsayin karamin sifiritanda (ASP) a shekarar 1995 inda da bisani ta zama kwamishina a shekarar 2016. Baju ta sai damar kamala Digiri na uku a jami’ar Plymouth a shekarar 2007. In da daga bisani ta zama mataimakiyar babban sifeton ‘yan sandan Nijeriya (AIG) a shekarar 2020 ta rike matakin kwamishina ‘yan sanda shugabar sashen dabbobi dake birnin tarayya Abuja.

  1. AIG Rhoda Adetutu Olofun:

AIG Rhoda Adetutu Olofun, ta fito daga Okene a jihar Kogi, itama tana daga cikin manyan ‘yan sanda da suka fito daga yankin Arewacin Nijeriya. Kamar waziri da Baju, takai matakin kwamishinan ‘yan sanda kafin daga bisani ta taka har zuwa matsayin mataimakin babban sifeton ‘yan sandan Nijeriya. Yanzu haka dai ita ce sakataren hukumar ‘yan sanda.

 Abin da bincike ya tabbatar: Wadannan jami’an ‘yan sanda mata da aka lisafta dukkanin su an daga likafarsu zuwa matakin kwamishinan ‘yan sanda kafin CP Hauwa Ibrahim, abinda aka fi sani dai shi ne DIG Aisha Abubakar Baju ita ce mace ta farko da ta fito daga ARewacin Nijeriya da aka fara daga likafarta zuwa kwamishinan ‘yansanda, kamar yadda yake a adane a Abusites shafin jami’ar Ahmadu Bello da aka sadaukar ga tsuffin dalibai

A TAKAICE:

Ikirarin da akayi na cewa CP Hauwa Ibrahim Jibrin ita ce mace ta farko kwamishinan ‘yan sanda daga arewacin Nijeriya ba gaskiya bane. Bincike ya tabbatar da cewa akwai kwamishinoni ‘yan sanda mata da suka fito daga ‘yankin na Arewacin kasar kafin ta, da suka hadar da AIG Farida Waziri, AIG Aisha Baju da kuma AIG Rhoda Adetutu Olufun.

Sai dai kuma, CP Hauwa Ibrahim ta kan iya zama mace ta farko da ta fara zama kwamishinan ‘yan sanda a jihar Kano.

PRNigeria

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HURIWA ta Soki Ƴan Sanda da NDPC Kan Jinkirin Binciken Zargin Kutse da aka yi wa Bayanan NIPSS da ya Shafi Jami’in Sojan RuwaƳa'yan El-Rufai Sun Shiga Rikici Yayin da Bashir ya Zargi Bello da Shan Muggan Kwayoyi da Cin Amanar suTsaro, Fafutuka da Nauyin Tabbatarwa Daga Mukhtar Ya’u MadobiONSA ta Fitar da Faɗakarwar Tsaro, ta Bukaci Ƴan Najeriya su ƙara Yawan Tsawaita TsaroHukumar DSS ta Dakatar da Shari'ar Sowore Kan Laifukan Intanet Har Sai Bayan Zaben Shugaban Kasa na 2027Gwarzo ya ba da Gudummuwar ₦10m ga Horarwa na Musamman na PRNigeria Bayan ya ba da Gidansa na Abuja Don Cibiyar Koyon Aikin Jarida2027: Bayan Takardu da Sauran Tsoffin Maganganu Marasa Amfani, ‘Yan Najeriya Sun Cancanci Kamfen Din da Ya Dace Da Matsaloli  Daga Kabir AkintayoGwamnati Tarayya ta Bayyana Bas 100 Masu Amfani da Wutar Lantarki Don Rage Wa Ma’aikatan Gwamnati Matsalar SufuriƳan Ta’adda na Amfani da Kafafen Sada Zumunta da Dandamalin Aikin Tura Kuɗi Don Tallafa Wa Ayyukansu — BukartiBinciken Gaskiya na PRNigeria: Ta Karyata Da’awar Tony Elumelu ta Cewa An yi Satar Man Fetur Kashi 97% Kafin Zamanin TinubuMeyasa Mutuwar Bazata Take Daukar Masu Alheri ta Bar Mugaye ? Na Yushau A. ShuaibSojoji Sun Kama Bindigar AK-103 Da Aka Boye a Cikin Jakar Gero, Sun Kama Mutum Uku A ZamfaraSojoji Sun Kama Shahararren Shugaban Ƴan Bindiga, 'Sanusi Maigilas' a Dajin Katsina2027: Yadda Zan Magance Rashin Tsaro, In Magance Matsalolin Tattalin Arziki da Zamantakewa a Kwara — Zakari MohammedLabarin NIPSS Mai Damuwa: Lokacin da Jami'in Sojan Ruwa Ya Cin Zarafin Mawallafi Daga Nuhu Mohammed
X whatsapp