Home General Majalisa ta buƙaci a kafa sansanin soji a yankin Bukuyum na Zamfara

Majalisa ta buƙaci a kafa sansanin soji a yankin Bukuyum na Zamfara

Majalisar wakilan Najeriya ta yi kira da a kafa sansanin soji a yankin Bukuyum sakamakon ƙamarin matsalar tsaro a yankin.

Ɗanmajalisar da ke wakiltar yankin, Sulaiman Abubakar Gumi ne ya gabatar da ƙudirin buƙatar hakan, inda ya ce ƴanbindiga sun mayar da yankinsa matsayin mafaka.

Ya ce suna tserewa yankin ne sakamakon yaƙarsu da ake yi a yankin Shinkafi da kuma sulhun da gwamnatin Kaduna ta yi da su.

Sojojin ƙasar dai sun ce suna ci gaba da luguden wuta kan ƴanbindiga, kuma sun ce suna samu nasara.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 6 Sun Rasu 4 Sun Jilkata Sanadiyyar Tsawa a Jihar AdamawaMatatar Dangote ta Dakatar da Amfani da Naira Wajen Sayar da Man FeturZaɓen 2027: Jam'iyyar ADC ta Mayar da Martani kan Hukuncin Kotu Akwai Yiwuwar ba zan kai Lokacin Zaɓen 2027 ba - ObiHukuncin da Kotu ta Yanke wa Direban Keke Napep Kan Aikata Fyaɗeɓata Sunan Gwamnatin Katsina: Kotu ta buƙaci Ƴan Sanda su Tsare Dr Kurfi Gwamnonin Arewacin Najeriya sun Kafa Gidauniyar Yaƙi da Matsalar TsaroGwamnatin Tarayya ba ta Yanke Hukuncin Sauya Kayan NYSC ba - Ministan MatasaJuyin Mulki: DSS ta Gurfanar da Mutane 5 kan ɓoye Timipre Sylva Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 2 Tare da Limami a Jihar Sokoto Dakarun Soji Sun Bankaɗo Wajen ƙera da Rarraba Bindigogi ga Ƴan Ta'addaJami'an DSS Sun Kama Tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche NnajiYan Bindiga Sun Hallaka Mutane 10 a Jihar BenueNMDPRA ta Gargaɗi Gidajen Man da ba su Rage Farashi ba NECO: ɗalibai 35 na Hannun Ƴan Bindiga - Ƴan Sanda 
X whatsapp