Home General Tinubu ya umarci a cire shingayen da ke kan iyakokin Najeriya

Tinubu ya umarci a cire shingayen da ke kan iyakokin Najeriya

Bola Ahned Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kafa wani kwamitin shugaban ƙasa na musamman da zai cire dukkan wasu shingaye da ake da su a kan iyakokin ƙasar don sauƙaƙa harkokin cinikayya da tafiye-tafiye.

Amabasada Musa Nuhu wakilain Najeriya a ƙungiyar Ecowas ne ya sanar da hakan, a wata ziyara da ya kai iyakar Najeriya da Jamhuriyar Binin wato Same a ranar Laraba.

Masu ababen hawa sun sha kokawa da yadda ake karɓar kudade a hannunsu, a dukkan wani shinge da suka zo wucewa akan hanayr ta Iyakar ta Seme wato iyakar Najeriya da jamhuriyar Benin.

Ambasada Nuhu ya ce “hanyar ta kasance wadda aka fi zirga-zirga a Afrika, musamman wajen fitarwa da shigar da kaya, da shige da ficen al’umma. Zamu iya ganewa idan ana tafiye tafiye ba tare da shinge ba a yankin Afrika ta Yamma”, in ji shi.

“Mun ji dukkan ƙorafe-ƙorafen da ake yi kan hanyar na yadda shingayen da jami’an tsaro da na jami’an hana fasa ƙauri ke sanyawa ke shafar matafiya da kayan da masu shigowa ko fitar da kaya.

Shugaban hukumar Ecowas Omar Alieu Touray ya yi, Allah wadai kan yadda jamai’an tsaron da ke kula da shingayen da ke hanyar ke ƙarɓar kuɗi a hanun al’ummar ƙasashe daban-daban da ke shige da fice a ƙasar, wanda ya ce hakan, ya saɓa da shirin ECOWAS na haɗe yankin wuri ɗaya

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp