Home DUNIYA An yi Musayar Fursunoni Tsakanin Rasha da Ukraine

An yi Musayar Fursunoni Tsakanin Rasha da Ukraine

Gwamnatin Ukraine ta sanar da yin musayar fursunoni sama da 100 tsakaninta da Rasha, musayar da ta ce ita ce ta farko da ta kunshi mata zalla, bayan shafe kusan watanni takwas suna gwabza yaki.

Shugaban ma’aikatar fadar shugaban Ukraine Andriy Yermak ya ce mata 108 suka samu nasarar kubutarwa yayin musayar fursunonin da suka yi da Rasha.

Yermak ya ce wasu daga cikin mutanen da aka yi musayar karbarsu daga hannun sojojin Rasha, iyaye ne da ‘yayansu mata da aka tsare su tare, yayin kawanyar da dakarun mamaya suka yi wa kamfanin sarrafa karafa na Azovstal da ke birnin Mariupol.

A cikin jawabinsa na yau da kullun da yammacin ranar Litinin, shugaba Vlodymyr Zelensky ya ce 96 daga cikin fursunonin da aka yi musanya sojoji ne mata, 12 kuma fararen hula.

Ita kuwa ma’aikatar tsaron Rasha ta ce mutanenta 72 da suka dawo daga Ukraine ma’aikatan wani jirgin ruwa ne na fararen hula da Ukraine ta tsare su tun a watan Fabrairu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp